BBC navigation

Bam ya hallaka mutane arba'in da shidda a Afghanistan

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:16 GMT
Harin bam a Afghanistan

Harin bam a Afghanistan

Mutane akalla arba'in da shidda ne suka mutu a wasu jerin hare- haren bam irin na kunar bakin wake a Afghanistan.

A lardin Nimroz dake kudu maso yammaci, an kashe akalla mutane talatin da shida, a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake suka tada wasu bama bamai.

Wasu mutane goma kuma sun mutu har wa yau a wani hari da aka kai a birnin Kunduz dake Arewacin Kasar.

Jami'ai na cewa akwai akalla wasu hare haren na kunar bakin wake takwas, wadanda aka hana aukuwarsu.

Shugaba Hamid Karzai dai ya yi Alah wadai da wadannan hare- hare, wadanda aka kai yayinda jama'a ke shirye shiryen bukukuwan sallah.

Galibin wadanda suka mutun fararen hula ne da suka hada da mata da kananan yara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.