BBC navigation

Mutane 33 sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa a Pilato

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:20 GMT
jos

Gadaje da dama sun rushe sakamakon ambaliyar

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane talatin da uku a jihar Pilato sakamakon ambliyar ruwa da aka yi a yankin kudancin jihar, baya ga gonaki da kuma gidaje da dama suka salwanta.

A cewar hukumomin, wasu mutanen fiye da dubu goma sha biyu kuma sun rasa muhallansu.

Kananan hukumomi da ambaliyar ta karshen mako ta fi shafa a jihar sun hada da; Wase da Kanam da Lantang ta Kudu da Langtang ta Arewa da Mikang da kuma Shendam.

Sakamakon ambaliyar dai, harkokin sufuri sun tsaya cik abinda ke kawo tsaiko wajen ayyukan bada agaji, kuma bayanai sun nuna cewar har yanzu mutane a yankin cikin mawuyacin hali.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta kasar- NEMA shiyyar arewa maso tsakiya Malam Abdussalm Muhammad, ya ce sun soma baiwa mutane a yankunan da abin ya shafa kayayyakin jin kai.

A 'yan makwannin da suka wuce ne akwai wani ambaliyar a birnin Jos lamarin daya raba mutane dubu uku da muhallansu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.