BBC navigation

An yi artabu tsakanin jam'ian tsaro a Yemen

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:32 GMT
yemen

Dakarun tsaro na sintiri a Yemen

Rahotanni daga Sana'a babban birnin kasar Yemen na cewa an yi taho mu gama tsakanin dakarun tsaro na musamman a kusada mai'akatar tsaron Kasar.

Dakarun tsaron na musamman na karkashin ikon dan tsohon shugaban Kasar Ali Abdullah Saleh ne, sun kuma fafata da wasu sojojin kasar.

An ruwaito cewar dakarun tsaron sun kaddamar da hari akan ma'aikatar tsaron, tare da yin amfani da manyan makamai.

Ganau sun ce sun ji karar harbin manyan bindigogi.

An kuma bada rahotan cewa dakarun tsaron na musamman sun karbe ikon babban bankin kasar.

A halin yanzu dai sabon shugaban kasar Abdrabu Mansur Hadi baya cikin kasar , yana halartar wani taro a can kasar Saudi Arabiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.