BBC navigation

An kai harin bam a birnin Maiduguri

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:20 GMT
Matakan tsaro a Maiduguri

Matakan tsaro a Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Najeriya sun ce mutane ukku ne suka hallaka, yayinda wasu biyu kuma suka samu raunuka ciki har da soja guda, sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a kan wata motar jami'an tsaro, a kusa da kasuwar Custom dake tsakiyar Maiduguri babban birnin Jihar.

Rundunar hadin gwiwar aikin samar da tsaro a jihar, JTF, ta ce dan kunar bakin waken ya rasa ransa.

A makwabciyarta, jihar Yobe kuwa an shafe sa'oi da dama ana musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da jami'an tsaro a tsakiyar Damaturu babban birnin jihar.

Rundunar JTF a yankin ta ce 'yan bindigar ne suka fara kai farmaki kan jami'anta dake aikin dauke gawar wani jami'insu da 'yan bindigar suka hallaka a daren jiya.

Jama'a dai na ci gaba da gudun hijira daga birnin Damaturu, a sakamakon fargabar barkewar rikici a birnin , lokacin bukukuwan Sallah.

Mutane da dama ne aka bada rahoton sun rasa na yi, a tashoshin mota, dauke da kaya, babu motocin sufuri da zasu kwashe su, zuwa wasu sassa na jihar ko wajen jihar.

Hukumomi na ci gaba da kira ga jama'a da su koma gidajensu, tare da ba su tabbacin kare su, da dukiyoyinsu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.