BBC navigation

An tsare wasu a Jamus kan shirin Nukiliyar Iran

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:44 GMT
Tashar Nukiliya ta Iran

Tashar Nukiliya ta Iran

'Yan sanda a Jamus sun tsare wasu mutane hudu da suke zargin suna kokarin fasakaurin kayayyakin nukiliya zuwa Iran.

Uku daga cikin wadanda aka tsaren nada takardun shedar zama yan Kasashen Jamus da kuma Iran din.

Ana zarginsu da yunkurin kai kayayyakin zuwa Iran ta hanyar kamfanonin bogi.

Iran dai na gina wata tashar makamashin nukiliya a kusa da garin Arak, kuma gwamnatocin kasashen yammacin duniya na fargabar za ta iya amfani da tashar wajen samar da makaman kare dangi.

Sai dai Iran tace shirin nukiliyar nata, na zaman lafiya ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.