BBC navigation

Akwai yiwuwar kai hari da salla a Maiduguri —JTF

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:29 GMT
Taswirar Najeriya mai nuna Maiduguri, Jihar Borno

Taswirar Najeriya mai nuna Maiduguri, Jihar Borno

Rundunar hadin gwiwa mai aikin samar da tsaro a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya, wato JTF, ta fitar da wata sanarwa da yammacin ranar Laraba tana nuni da yiwuwar kai wadansu hare-hare a kan jami'an soji da fafaren hula a lokutan bukukuwan sallah.

Saboda haka ne ma ta ce za ta sake daukar wadansu sababbin matakai domin dakile wannan yunkuri.

Wannan sanarwa ta fito ne sa’o’i kadan bayan wani harin kunar-bakin-waken da ya hallaka mutane biyu tare da jikkata wadansu uku, ciki har da jami'an soja a tsakiyar Maiduguri, babban birnin jihar.

A Damaturu babban birnin Jihar Yobe mai makwabtaka ma, jama'a na ci gaba da kaura sakamakon yawan kai hare-hare da musayar wutar dake faruwa tsakanin jami'an tsaro da ’yan bindiga.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.