BBC navigation

Wani bam ya tashi a tsakiyar birnin Damascus na Syria

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:07 GMT
Wani harin bam a D amascus na Syria

Wani harin bam a D amascus na Syria

Wani bam da ya tashi a tsakiyar Damascus babban birnin Syria, ya raunata mutane akalla 5 a kusa da wani Otel da masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya ke amfani da shi -- sai dai babu daya daga cikinsu da ya jikkata.

Sojin yan adawa na Free Syria sunce harin bam din ya nufi wani taron manyan hafsoshin soji ne.

Masu fafutika sun bayar da rahoton cewar artabu ya kaure tsakanin mayakan yan tawaye da dakarun gwamnati a kusa da Ofishin Pirayim Minista da kuma Ofishin Jakadancin Iran, to amma ba a tabbatar da wannan ba.

Kungiyar kare hakkin Bil adama ta Human Rights Watch ta ce tana da shedar cewar wani jirgin saman yakin Syria ya harba makamai masu linzami a wani asubiti a yankin Allepo da yan tawaye ke rike da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.