BBC navigation

Saudi Arabia ta nemi 'ya'yanta su bar Lebanon

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:57 GMT
Wani harin bam a D amascus na Syria

Wani harin bam a D amascus na Syria

Saudi Arabia ta bukaci dukkanin 'yan kasar ta dake Labanon su bar kasar nan take, bayan barazanar da wata haula ta ’yan Shi'a ta yi cewa za ta sace su.

Iyalan Al Miqdad sun yi wa ’yan kasashen Saudi Arabia da Qatar da Turkiyya barazana da kuma dukkanin kasashen Musulmi ’yan Sunni dake goyan bayan ’yan tawayen Syria.

Haular dai ta yi garkuwa da wadansu Syriyawa a Labanon, wadanda ta ce suna da alaka da ’yan tawaye.

A halin da ake ciki kuma, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce dakarun gwamnatin Syria sun aikata laifuffukan cin zarafin jama'a wadanda suka hada da kisan fararen hula fiye da dari a kauyen Houla a cikin watan Mayu.

A wani rahoto da suka fitar, masu binciken sun ce kungiyoyin ’yan tawaye ma sun aikata laifuffukan yaki wadanda suka hada da kisa da azabtarwa.

Rahoton, wanda ya duba abubuwan dake faruwa tun daga watan Fabrairu har zuwa watan Yulin bana ya nuna cewa a tsawon wannan lokacin, rikicin ya bazu zuwa wadansu sassa na kasar; Majalisar ta kuma dora alhakin hakan a kan dukkan bangarorin.

An aikata laifukan yaki a Syria

Haka kuma an kammala rahoton da cewa dakarun sojin Syria ne ke da alhakin kisan gillar da ya faru watanni uku da suka gabata a kauyen Houla, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a kasashen duniya.

Rahoton ya ce yara arba'in da tara na cikin mutane darin da suka rasa rayukansu yayin kisan gillar, wanda dakarun sojin Syria da ’yan ta'adda masu goyawa gwamnati baya suka jagoranta.

A bangare daya kuma, Kungiyar Kasashen Musulmai na gudanar da taron gaggawa a kasar Saudi Arabia,don cimma matsaya a kan korar Syria daga kungiyar.

Sarki Abdallah na Saudi Arabia ya yi kira ga kasashen Musulmi su dauki matsayi na bai-daya.

“Duniyar Musulunci tana cikin wani yanayi na rashin fahimtar juna da kuma sabani, kuma ana zubar jinin Musulmi da dama a cikin wannan wata mai alfarma a sassa daban daban na duniya.

’Yan uwana Musulmi, abu mafi a'ala shi ne hadin kai da lamuntar juna da kuma sassauci a tsakanin al'umar Musulmi”, inji Sarki Abdallah.

Kasar Iran dai na adawa da wannan yunkuri, kuma Shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad na halartar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.