BBC navigation

'Yan sanda sun yi arangama da masu zanga zanga a Gabon

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:21 GMT

Adre Mba da magoya bayan sa

Jami'an 'yan sanda da magoya bayan 'yan adawa sun yi arangama a kasar Gabon da ke Yammacin Afrika.

Shugabannin jam'iyyar adawa ta National Union sun ce an kashe mutane uku tare da jikkata wasu talatin yayin wata zanga-zanga a Libreville, babban birnin kasar.

Sai dai jami'an gwamnati sun ce babu wanda ya rasu kuma mutane kalilan ne su ka jikkata.

Masu zanga-zangar na nuna goyon bayansu ne ga tsohon dan takarar shugaban kasar, Andre Mba Obame wanda ya koma Gabon a karshen makon jiya bayan gudun hijirar watanni goma sha hudu a Faransa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.