BBC navigation

Ministan Shara'a na Najeriya ya nemi a dakatar da rusau a unguwar Mpape dake Abuja

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:46 GMT
Mohammed Bello Adoke Ministan Shara'a na Najeriya

Mohammed Bello Adoke Ministan Shara'a na Najeriya

Mahukunta babban birnin Tarayya Abuja sun fara rusa wasu gine-gine da suka ce an yi su bisa ka'ida ba a Unguwar Mpape dake birnin tarayya.

Tun da farko da mahukunta babban birnin tarayyar sun baiwa mazauna unguwar da suka yi gine gine ba bisa ka'ida ba wa'adin nan da karshen watan Ogusta ne da su tashi daga gidajen nasu.

Yanzu haka dai jama'a da dama dake unguwar sun shiga wani hali na rudani sakamakon rushe rushen da mahukuntan birnin suka fara aiwatarwa a unguwar.

To a halin da ake ciki kuma tuni Antoni Janar kuma ministan shari'ar kasar, Mohammed Bello Adsoke, ya shawarci ministan babban birnin tarayyar Abuja da ya dakatar da shirin rusau a yankin na Mpape har sai an kammala sauraron shari'ar da al'ummar yankin suka shigar a gaban kotu.

Wata wasikar da aka aika wa ministan Abuja, ta ce ma'akatar shari'a ta yi nazarin koken da aka shigar a gabanta game da batun, don haka Ministan shari'ar yake shawartar takwaransa na Abuja da ya dakatar da aikin rusau din don yin biyayya ga tsarin shari'a kamar yadda gwamnatinsu ta yi alkawarin aiwatarwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.