BBC navigation

OIC ta dakatar da wakilcin Syria

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT

Taron OIC

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi, OIC, ta dakatar da wakilcin kasar Syria.

A karshe taron kungiyar a birnin Makka mai alfarma na kasar Saudi Arabia, Sakatare Janar na kungiyar Ekmeleddin Ihsanoglu ya ce kungiyar ba ta da gurbi ga duk gwamnatin da ke kashe mutanen ta.

Yace wannan muhimmin sako ne ga gwamnatin Syria cewa duniyar musulunci ba ta amince da tsarin da ke kashe al'umma ba. Haka kuma sako ne ga kasashen duniya cewa al'ummar Musulmi na goyon bayan sauyin shugabanci cikin lumana kuma ba ta son cigaba da zubar da jini.

Rikicin Syrian dai dada kazanta ya keyi inda ake ci gaba da artabu tsakanin dakarun gwamnati da kuma na 'yan tawaye.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.