BBC navigation

An kai farmaki kan wani sansanin mayaka a Pakistan

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:11 GMT
Matakan tsaro a Pakistan, bayan hari

Matakan tsaro a Pakistan, bayan hari

'Yan gwagwarmaya a Pakistan sun kai hari a kan daya daga cikin manyan sansanonin jiragen sama na kasar.

'Yan bindigar sanye da kayan soji, kuma dauke da bindigogi masu sarrafa kansu da gurneti gurneti sun shiga cikin sansanin a Kamra kusa da Islamabad babban birnin kasar ne, gabanin asubahi.

Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban a Pakistan ya ce sune suka kai harin.

An kashe 'yan gwagwarmayar takwas, da soji daya a artabun da aka shafe dogon lokaci ana yi da bindigogi.

Akalla dai jiragen saman yaki talatin ne ne ke a sansanin, to amma daya ne kawai ya samu lahani.

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da 'yan Taliban suka kai sansanin soji a 'yan shekarun nan.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.