BBC navigation

Dangantakar Birtaniya da Ecuador ta yi tsami

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 05:22 GMT

Julian Assange


Dangantaka ta kara tsami tsakanin kasar Birtaniya da kasar Ecuador kan makomar Julian Assange, wanda ya kirkiri shafin internet na Wikileaks.

Mr Assange, wanda ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Ecuador dake birnin London watanni biyu da suka wuce ya samu izinin mafaka a Kasar.

Ana kokarin tusa keyarsa ne zuwa kasar sweden kan zargin da ake masa na laifukan da suka shafi jima'i amma ana tsoron ko za aika shi zuwa kasar Amurka inda ake neman sa ruwa a jallo.

Shekaru biyu da suka wuce Shafin Wikileaks ya buga dubban bayanai na sirrin kasar Amurka.

Minitan harkokin waje na Ecuador Ricardo Patino ya ce sun amince su bawa Mr ssange mafaka a kasar.

A bangare guda kuma kasar Birtaniya ya zama wajibi su tusa keyar Mr Assange zuwa sweden saboda bai samu nasarar ba a duk karar da ya daukaka.

Wannan kiki-kakar tsakanin kasashen biyu na dada sa dangantakar su ta kara tsami.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.