BBC navigation

Dattawan Borno sun sake mika kukensu

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:26 GMT
Rikicin a rewcin Najeriya

Rikicin a rewcin Najeriya

Kungiyar Dattawan Yankin Borno da ke arewacin Najeriya, ta sake yin kira ga dukan masu ruwa da tsaki a tashin hankalin da ya addabi yankin da su sake tunani su yi hakuri su ajiye makamai domin samun hanyar sasantawa.

A wata sanarwar da kungiyar ta fitar bayan wani taro da ta yi a Maiduguri, babban birnin jahar Borno, ta bukaci jami'an tsaron hadin guiwa dake aikin tabbatar da tsaro a yankin da su sake salon yadda suke tinkarar lamarin.

Jama'a da dama a biranan Maiduguri da Damaturu na zargin jami'an tsaron a jahohin da aikata kisan kiyashi, a duk lokacin da suka kama matasa da mutanan da ba su ji ba su gani ba.

Lamarin da yasa a yanzu haka jama'a ke ta yin kaura suna barin garuruwansu.

A nata bangaran rundunar tsaro ta hadin guiwa a jahar Borno ta musanta dukkan zargin da jama'a ke yi na aikata kisan kiyasi a jahar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.