BBC navigation

Indiya ta yunkura ga kawar da jita jitar afkuwar tashin hankali

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:20 GMT
Baki  yan ci rani a India

Baki yan ci rani a India

Gwamnatin India ta bullo da wasu matakai na gaggawa a wani kokari na dakatar da tserewar da dalibai da kuma ma'aikatan cirani suke yi daga arewa maso gabashin kasar

A rana ta uku dai dubun- dubatar mutane na tserewa daga manyan birane saboda fargabar jita- jitan da ake ta yadawa, cewa za a sami tashin hankali

Gwamnatin India ta kakaba dokar haramta aikewa da sako ta waya na text zuwa fiye da mutun biyar a lokaci guda, domin dakile irin wadannan jite- jiten

Prime Ministan Kasar Manmohan Singh, ya yi kira da a kwantar da hankula.

Ana dai danganta kidimar da mutane suke yi da yiwuwar kadddamar da hare- haren ramuwar gayya, saboda riikicin dake cigaba da gudana tsakanin kungiyoyin kabilu a Assam

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.