BBC navigation

Yansandan Afrika ta Kudu sun kashe masu hakar ma'adinai 34

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:15 GMT
Yansandan Afrika ta Kudu

Yansandan Afrika ta Kudu

Hukumar 'Yan sandan Kasar Afirka ta Kudu ta ce an kashe mutane talatin da hudu a lokacin da jami'an 'yan sandan kasar suka bude wuta kan dubun- dubatar ma'aikatan hakar ma'adinai dake yajin aiki a ranar alhamis, kuma hakan shi ne wani yanayi mafi muni da aka taba gani tun lokacin da aka kawo karshen zamanin wariyar launin fata

'Yan sandan sun ce matakin da suka dauka na kare kansu ne.

Babbar jami'ar yansandan Kasar ta ce, 'yan sanda sun zagaye yankin, kuma sunyi yunkurin tarwatsa masu zanga zangar da harsashen roba, amma suka yi kansu da manyan makamai, abinda ya tilasatawa 'yan sandan kare kansu

An tsare mutane sama da dari biyu da hamsin, Kuma kungiyoyin ma'aikatan sunyi kira da a gudanar da bincike

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.