BBC navigation

Kisan masu hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 13:39 GMT

Kisan mahaka platinum talatin da 'yan sanda suka yi a Afirka ta Kudu, a zubar da jini mafi muni tun bayan kawo karshen mulkin tsiraru farar fata, ya jawo takaici da takaddama a kasar. Editan BBC a kan al'amuran da suka shafi Afirka, Martin Plaut, wanda ya taba kai ziyara mahakar, ya duba dalilan da suka haddasa wannan asarar rayuka.

Masu hakar ma'adinan da ke yajin aiki a Afirka ta Kudu

Masu hakar ma'adinan da ke yajin aiki a Afirka ta Kudu

Yankin arewa maso yammacin Afirka ta Kudu, wanda fako ne, a kunshe yake da ma'adinar platinum mafi girma a duniya.

A can karkashin kasa, ma'aikata kan hakokin ma'adanin cikin wani mummunan yanayi, inda maza majiya karfi kan shafe sa'o'i da dama suna sarrafa na'urar huda kasa mai nauyin kilo ashirin da biyar.

Wadannan mahaka tsiraru ne--saboda zababbu ne a cikin majiya karfi.

Bukatar wadannan ma'aikata ta karin albashi ce dai ta haddasa yajin aikin da suka fara yi; har ma suka dauki adduna da masu--abin da ke nuna ba sani ba sabo.

Sai dai kuma matsalar ta wuce haka.

Kungiyar kwadagon da ta fi karfi a yankin, wato NUM, muhimmiyar kawa ce ga jam'iyyar ANC mai mulki.

Saboda haka, goyon bayan kungiyar na da muhimmanci ga Shugaba Jacob Zuma a yunkurinsa na kankame mukaminsa na shugabancin jam'iyyar yayin zaben da za a gudanar a watan Disamba.

Masu hakar ma'adinan dai suna zargin shugabanninsu da yin watsi da batutuwan da ke damun al'umma da mayar da hanakali fiye da kima a kan al'amuran siyasa.

Kwatar hakkoki

Saboda haka suka mayar da kansu wata kungiya ta daban da nufin kwato hakkokinsu.

"'Yan sanda dubu ukun da suka kewaye tudun da masu hakar ma'adinan suke kuma ba sa sha'awar bin sahun abokan nasu biyu."

Amma, kamar yadda aka sha gani a Afirka ta Kudu, sai al'amarin ya rikide ya zama tashin hankali.

Tun a farkon mako dai 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu.

'Yan sanda dubu ukun da suka kewaye tudun da masu hakar ma'adinan suke kuma ba sa sha'awar bin sahun abokan nasu biyu.

Wannan tamkar wata al'ada ce ta rundunar 'yan sandan.

Kamar yadda wani tsohon kwamishinan 'yan sanda ya ce su kan yi harbi da nufin kisa ba tare da damuwa da abin da ka biyo baya ba.

Masu sharhi a Afirka ta Kudu dai na kwatanta wannan bala'i da al'amarin Sharpeville wanda ya haifar da fafutuka da makamai, lokacin da 'yan sanda suka yi harbi a kan jama'a a shekarar 1960.

Ga alama wannan kwatance ya wuce gona da iri, amma kasar na fuskantar wani yanayi mafi muni tun bayan mulkin wariyar launin fata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.