BBC navigation

An kashe masu hako ma'adanai a Afrika ta Kudu

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 05:15 GMT

Yan sanda a Afrika ta kudu na farma masu zanga zanga

'Yan sandan Afrika ta kudu sun bude wuta kan dubunnan ma'aikatan hakar ma'adinai da ke yajin aiki, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawa, a rikicin mafi muni a kasar tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.

Wani da abin ya faru a gabansa ya shaidawa BBC cewa ya kirga gawarwaki goma sha takwas daura da mahakar ma'adinin Platinum da ke nisan kilomita dari arewa maso yammacin Johannesburg.

Yace 'yan sandan sun bukaci masu yajin aikin da su ajiye makamansu da suka hada da adduna, da masu da kuma kulake.

Yayinda suka kasa fasa taron da hayaki mai sa hawaye da kuma bututun ruwa sai suka bude wuta tsawon mintuna biyu.

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma yace hankalinsa ya tashi kuma ya yi matukar takaicin asarar rayukan da aka yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.