BBC navigation

An yi zanga-zangar kyamar Japan a China

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:00 GMT
Masu zanga-zangar kyamar Japan a China

Masu zanga-zangar kyamar Japan a birnin Jinan na China

An gudanar da zanga-zangar kyamar Japan a wadansu biranen China bayan da wadansu masu fafutuka ’yan kishin kasa na kasar ta Japan suka kafa tutar kasarsu a wadansu tsibirai da ake takkadama a kansu.

Dubban mutane ne dai suka gudanar da zanga-zangar a birane akalla takwas don nuna adawa da matakin na ’yan kishin kasa na Japan.

A Shenzhen, da Guanzhou, da sauran birane, masu zanga-zanga dauke da tutocin China sun bukaci Japan ta janye daga tsibiran.

Wadanasu masu zanga-zangar a Shenzhen ma har motoci da sauran kayayyaki kirar Japan da ma gidajen cin abinci mallakar ’yan kasar Japan suka lalata.

Kafa tutar Japan da masu fafutkar suka yi a tsibiran da ake kira Senkaku a Japan ko Diaoyu a China, ita ce ta baya-bayan nan a jerin takaddamar da ke kara haifar da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen biyu a kan mallakar yankuna.

Masu fafutukar su goma da suka yi iyo suka kafa tutar bangare ne na wani ayari da ya je tsibiran a jirgin ruwa.

'Wajibi ne a samu wanda zai aikata haka'

Gwamnatin Japan—wacce ke iko da tsibiran—ta hana su izinin zuwa wurin, kuma masu gadin gabar tekun kasar sun yi musu tambayoyi.

A makon da ya gabata dai wadansu masu fafutuka ’yan China sun saci jiki sun je daya daga cikin tsibiran, inda suka kafa tutar China.

Wani dan majalisar dokokin Japan, Eiji Kousaka, na cikin mutanen da suka je tsibiran, ya kuma ce hakki ne da ya rataya a wuyansa ya mayar da martani ga wannan takalar fadan.

“Wannan wani abu ne da ya wajaba a samu wani ya aikata shi, musamman ma tunda ranar 15 ga wata wasu da suka kira kansu masu fafutuka ’yan China suka mamaye daya daga cikin tsibiran—wa ya sani ma ko akwai sojoji a wurin. Don haka ba zan zura ido kawai in tafi kamun kifi ba”, inji Mista Kousaka.

’Yan majalisar dokoki biyu ne dai suka shiga cikin ayarin na ’yan ksishin kasa na Japan, suna masu cewa yana da muhimmanci kasar ta Japan ta fito fili ta nuna wanda ya mallaki tsibiran.

Tuni dai China da Taiwan—wacce ita ma take ikirarin mallakar tsibiran—suka nuna rashin jin dadinsu da faruwar wannan al'amari ga Japan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.