BBC navigation

Igiyar teku ta yi awon gaba da mutane 15 a Najeriya

An sabunta: 18 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 21:02 GMT

Gidajen da ambaliyar ruwa ta share a arewacin Najeriya

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Jihar Legas da ke Najeriya ta ce tana can tana neman wadansu mutane goma sha biyar wadanda suka bata bayan wata igiyar teku ta yi awon gaba da su.

Akalla mutun daya ya mutu bayan da igiyar tekun ta afkawa al'ummomin da ke zaune a unguwar Kuramo Beach dake gabar tekun Atlantika a birnin na Legas.

A daren ranar Juma’a ne dai igiyar ruwan ta mamayi unguwar ta marasa galihu lokacin da mutane ke barci.

Shugaban hukumar, Olufemi Oke, ya shaidawa BBC sun killace wurin, sannan ya kara da cewa:

“Da faruwar al’amarin, sai muka tayar da dukkan na’urorinmu na bayar da agajin gaggawa, kuma dukkan wanda ke da ruwa datsaki a al’amarin yana wurin”.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.