BBC navigation

Dan sanda ya kashe yaro a Kano

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 05:53 GMT
Yan sandan Najeriya

Yan sandan Najeriya

Wani dan sanda da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ya harbe wani yaro mai kimanin shekaru 11 wanda ya mutu har lahira.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da ofishin 'yan sanda na Gwale da yammacin Asabar, abinda kuma ya harzuka mazauna yankin.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce tuni ta dauki matakin ladabtarwa ga jami'in na ta.

A baya dai 'yan sanda a Najeriya sun sha hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Hukumomin 'yan sanda kan cewa su na ladabtar da wadanda ke aikata kisan tare da sallamarsu daga aiki, sai dai hakan ba ya hana sake afkuwar lamarin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.