BBC navigation

Musulmi na bikin sallah karama

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 03:59 GMT
Musulmi na Sallah

Musulmi na Sallah

A yau ne Musulmi a fadin duniya ke bukukuwan sallar Eid el-Fitr wadda aka fi sani da karamar sallah.

Ana wadannan bukukuwan ne bayan kammala azumin watan Ramadan.

Tun a jiya ne dai wasu kasashen da suka hadar da Nijar, da Pakistan da Afghanistan suka yi tasu sallar domin sun ce sun ga wata.

A kasashe irinsu Najeriya, Saudi Arabiya da Hadaddiyar Daular Larabawa kuwa, shugabanni sun ce ba su samu rahoton ganin wata ba, a don haka suka bada umarnin a cika azumin watan Ramadana kwanaki talatin.

A lokaci irin wannan Musulmi kan yi kwalliya su je Sallar Idi domin raka'a biyu ta nafila.

Bayan nan ne kuma suke ci gaba da taya juna murna ta hanyar ziyarce-ziyarce da kuma wasu nau'o’in nishadi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.