BBC navigation

Babban jami'in sojin Amurka ya tsallake rijiya da baya

An sabunta: 21 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:28 GMT
Martin Dempsey

Martin Dempsey ya kai ziyara ne ga sojojin Amurka a Afghanistan

Rokokin da wasu 'yan bindiga a Afghanistan suka harba akan wani sansanin sojin Amurka sun yi sanadiyyar lalata jirgin da babban jami'in rundunar sojin Amurka Janar Martin Dempsey ke amfani da shi.

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce anyi sa'a ma Janar din baya kusa, a lokacin da aka harba rokokin.

Kuma babu wanda ya samu rauni a sakamakon hari.

Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki nauyin kaddamar da harin.

Janar Dempsey ya kasance a sansanin sojin saman Bagram, domin tattaunawa kan yawan hare- haren da 'yan Afganistan din suke kaddamarwa a kan sojojin kasashen duniya.

Sai daga bisani Janar din ya samu ya fice daga sansanin a cikin wani jirgin daban.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.