BBC navigation

Tarihin shugaba Meles Zenawi

An sabunta: 21 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:58 GMT
Meles Zenawi

An yabawa Meles Zenawi kan rawar da ya taka wurin farfado da tattalin arzikin kasar

Mr Meles ya fito daga gidan dake da rufin asiri a garin Adawa a Tigray dake arewacin kasar.

Kuma ya dakatar da karatunsa na jami'a, inda ya fada harkokin gwagwarmaya.

Mista Meles mutum ne mai tsantseni da kuma kwazo, ya dinga sa ido sosai a kan al'amuran gwamnati, kuma baya sassauci game da duk wata alama ta rikicin cikin gida a jam'iyyarsa.

Kazalika mutum ne shi mai basira ga iya magana.

Ya auri wata gogaggiyar 'yar siyasa a jam'iyyar TPLF kuma 'yar kasuwa sannan 'yar majalisa, Azeb Mesfin.

Sun haifi yara uku da ita kuma sun tafiyar da rayuwarsu ta madaidaiciyar hanya, a wani dan karamin gida a Adis Ababa.

Mr. Meles, mutum ne mai son buga wasan tenis, kuma ba ya zuwa hutu, haka kuma kusan kodayaushe fuskarsa a murtuke.

Lokacin da aka taba ganin ya saki jiki ya yi murmushi shi ne, lokacin da kasar ke murnar cika shekaru dari.

Sanye da kayan gargajiya ya yi rawa da maidakinsa, sakin jikin da ya yi ya zama abin magana a kasar.

Siyasa

Meles Zenawi dan siyasa ne mai azanci da jam'iyyar Tigray People's Liberation front ta taba samu.

TPLF na daga cikin kungiyoyin da suka jagoranci gwagwarmayar adawa da gwamnatin mulkin soja a Habasha a shekarun 1970 zuwa 1980.

Bayan an kifar da gwamnatin Mengistu Haile Mariam a shekarar 1991, Mista Meles ya zama shugaban rikon kwarya na farko na Habasha.

Sannan a shekarar 1995 ya zama Firai Minista.

Ethiopia

Kasar Habasha ta sha fama da matsalar mummunan karancin abinci

Tun daga nan ne kuma ya mamaye zukatan 'yan kasar Habasha.

Gwamnatinsa ta fuskanci wasu kalubale, ciki har da ballewar yankin arewacin kasar wato Eritea.

An zargi Mista Meles Zenawi da rabuwa da yankin cikin ruwan sanyi.

Sannan yakin bakin iyaka ya biyo baya, kodayake Habasha ta samu nasarar yakin, amma ta tafka asara.

Firai ministan ya maida masu sukarsa a jam'iyyarsa saniyar ware, abin da ya kara masa karfi.

Ayyukansa

Za'a iya tuna Mista Zenawi da shekarun da ya kwashe a lokacin gwagwarmaya.

A karkashin shugabanci sa ne kasar habasha ta fara bude kofofinta ga kasashen duniya.

Kuma duk da akidarsa ta gurguzu ya yarda masu zuba jari na kasar waje su shiga kasar, musamman a bangaren noma da kiwo.

A dan wani lokaci Mr. Meles ya zama abokin kasashen duniya, inda suke jinjina masa game da maida hankali kan cigaban yankunan karkara, sannan kusan babu cin hancin da rashawa a gwamnatin sa.

kuma ya zamo abokin Amurka a kan batun yaki da ta'adanaci.

Sai dai ya dauki tsauraran matakai na takurawa 'yan adawa bayan su yi abin a zo a gani a zabukan shekarar 2005.

Kuma a baya-bayan nan an diga amfani da dokar yaki da ta'addanci wajen muzgunawa 'yan jarida da masu yada bayanai ta intanet da sauran masu sukar gwamnati.

Haka kuma wani yunkuri na nuna ikon gwamnati har a masallatai ya sa Musulmai sun yi zanga-zanga a titunan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.