BBC navigation

Ethiopia ta samu sabon Fira minista

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:44 GMT

Jami'an gwamnati suna cire wani hoto na Meles Zanawi bayan bayyana mutuwarsa

Mataimakin Meles Zanewi Hailemariam Desalegn ya gaje shi a zaman Fara ministan Ethiopia bayan rasuwarsa ranar litinin.

Desaleng wanda ba kowa ne ya san shi ba dai, zai gudanar da gwamnatin kasar ne har zuwa lokacin zabe a shekara ta 2015.

An dai haifi Hailemariam Desalegn ne a shekarar 1965 kuma ya fito ne daga kabilar Wolaita dake a kudancin kasar.

A farkon shigarsa cikin harkokin siyasa ya rike mukamin shugaban daya daga cikin larduna tara da kasar keda da aka fi sani da Southern Nations, Nationalities and People's Region (SNNPR).

Mataimaki mai biyayya

An nada shi mukamin babban minista a shekara ta 2008. Jam'iyyarsa ta EPRDP tana daga cikin kawancen jam'iyyun da ke mulkin kasar.

A watan Oktoban 2010 Meles Zanawi ya nada shi mukamin mataimakinsa kuma ministan harkoki wajen.

A wani lokaci jaridar Indian Ocean ta baiyana shi da ''abokin kawance mai biyayya ga Meles, wanda baya sakaci da duk wata dama da ya samu ta kare matsayi da kimar shi Meles Zanawi din''.

Wani shafin na'urar internet na 'yan adawa Addisnegronline.com yace an nada shine domin zama dan-amshin-shata ga manufofin faraministan.

Wani shafin internet din na 'yan adawa dake a Amurka Nazret.com ya fi rage masa kima, inda ya kira shi dan kwikwiyon da melez ya sayo.

Wani mai sharhi ya bayyana Mr. Haile Mariam a zaman mutum mai rangwamen muruwar shugabanci, inda yace zai fi kyau ga zama mataimaki bisa ga zama shugaba.

Yankin da ya fito dai yana tasiri ga kallon da ake masa.

Ko da yake dai kawancen jam'iyyun larduna ne ke jagorantar kasar ta Ethiopia, Jam'iyyar TPLF daga lardin Tigray na arewacin kasar itace ke rike da ainihin madafun ikon kasar, a cikin rundunar soji da kuma a gwamnati.

Da yake Mr. Haile Mariam ya fito ne daga daya daga cikin yankunan da ake dasu a kudancin kasar wadanda ba suda tasiri a siyansace, masu sharhi ne cewar wannan zai sa ya zama abu mai wuya ya cigaba da rike mukamin nasa idan 'yan lardin Tigray wadanda ba su son mulki ya kubuce musu; ko kuma 'yan siyasa daga wasu larduna masu tasirin siyasa dake jin an dade ba a damawa dasu suka kalubalance shi .

Mr. Haile Mariam dai yana shugabantar kamfunna da dama mallakar Gwamnati.

Yayi karatun digiri na daya a fannin injiniyanci a jami'ar Addis Ababa da kuma digiri na biyu daga jami'ar Finland.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.