BBC navigation

Girka ta nemi karin lokacin aiwatar da sauye-sauye

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT

Fara minista Antonis Samaras yana hira da 'yan jarida a Athens

Fara Ministan Girka Antonis Samaras ya sake yin kiran da a ba shi karin lokaci da zai zaftare adadin kudin da gwamnati ke kashewa da kuma aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

Takwarorin kasar ta Girka a Tarayyar Turai sun dage a kan sai lallai ta zaftare kudin da take kashewa a matsayin wani sharadi na cigaba tallafawa kasar da bashi ya yiwa katutu.

A hirar su da wata Jarida ta kasar Jamus, Antonis Samaras ya ce, Girka na bukatar karin lokaci na farfado da tattalin arzikinta.

Nan gaba ne a yau Laraba, zai gana da jagoran Ministocin kudi na kasashen Tarayyar Turai Jean Claude Junckera birnin Athens.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.