BBC navigation

Antonis Samaras zai gana da shugabannin Turai

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:21 GMT
Antonis Samaras

Firayim Ministan Girka, Antonis Samaras

Yayin da yake shirin fara wata tattaunawa ta kwanaki uku da nufin karbo kashi na gaba na tallafin kudi ga kasarsa, Firayim Minista Antonis Samaras ya ce Girka na bukatar a sakar mata mara don ta samu damar farfado da tattalin arzikinta.

Mista Samaras ya ce zai nemi a karawa kasar ta Girka lokaci don farfado da tattalin arzikin nata yayin wata ganawa da zai yi da shugaban taron ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudin euro Jean-Claude Junker.

Wannan tattaunawa dai daya ce daga cikin muhimman tattaunawa uku da Mista Samaras zai yi a cikin wannan makon.

Zai tattauna da shugabannin Faransa da Jamus

Zai tattauna da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin ranar Juma'a, daga bisani kuma zai gana da Shugaban Faransa Francois Hollande ranar Asabar.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne a kan shirye-shiryen Girka na zabtare kudaden da ta ke kashewa da euro miliyan goma sha daya da dubu dari biyar, tana fatan hakan zai sa ta samu kudaden da za su ceto tattalin arzikin ta nan gaba.

Mista Samaras ya ce zai tabbatar wa kasashen da ke amfani da kudin euro alkawarin da Girka ta yi tare da fito da wadansu sababbin hanyoyi don farfado da arzkin kasar

Ya kara da cewa Girka ta fuskanci matsala saboda zaben da aka gudanar a bana, don haka sai a hankali kasar da mutanenta za su farfado daga radadin da suka shiga.

A farkon wannan makon dai shugabannin kasashen Turai sun tabbatar da cewa sun duba yiwuwar ficewar Girka daga sahun kasashe masu amfani da kudin euro.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.