BBC navigation

Za a auna kwazon Ministoci a Najeriya

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:34 GMT
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya,ministocin kasar suka rattaba hannu a kan wata takardar auna kwazonsu wajen gudanar da ayyukan ma'aikatunsu.

Majalisar zartarwar kasar ta ce sabon tsarin zai taimaka wajen kara wa ministocin azama.

Sai da majalisar zartawa ta kasar da Shugaban kasar suka amince da sabon tsarin auna kwazon ne dai kafin kaddamar da shi.

Ma'aikatar tsare tsare ta kasar ce ta shirya wannan ma'auni wanda gwamnati ta ce zai taimaka wajen samar da sauyi ga yadda ake tafiyar da kasafin kudi a kasar.

Ma'aikatar tsare tsaren ta nuna damuwa ga yadda a baya ma'aikatu kan kare yadda suke kashe kudaden da ake kebe masu a kasafin kudi ta hanyar tafiye tafiye da shirya taruka wadanda ba za a iya nuna zahirin yadda za su shafi rayuwar al'umar kasar ba.

Bangaren zartarwa a Najeriyar dai na shan suka daga 'yan kasar da dama kasancewar ba ya aiwatar da kasafin kudi yadda ya kamata.

A 'yan kwanakin nan ma sai da majalisar dokoki ta bai wa shugaban kasar wa'adi domin ya aiwatar da kasafin kudin wannan shekarar, ko su kwashi 'yan kallo.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.