BBC navigation

Gwamnonin arewa a Najeriya sun kafa kwamitin tsaro

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:32 GMT

Taswirar Najeriya

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti da nufin magance matsalar rashin tsaro dake karuwa a yankin.

Kwamitin na samar da zaman lafiya ya hada da Sarakunan gargajiya da shugabannin addini da sojojin da suka yi ritaya da ’yan kasuwa da kuma tsofaffin ma'aikatan gwamnati.

Hare-haren da kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah lid-Da’wati wal Jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram, ke ci gaba da kaiwa a arewacin kasar dai na jawo tabarbarewar tattalin arziki a yankin.

Wannan ne dai karo na farko da gwamnonin suka kaddamar da irin wannan kwamiti.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.