BBC navigation

Attajirai a China na sayen gidaje a kasashen waje

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:39 GMT
Louie Huang

Louie Huang, wani attajiri a kasar China

Attajirai a kasar China na neman izinin mallakar gidaje a kasashen ketare, domin rashin tabbas game da manufofin gwamnatin kasarsu.

Louie Huang wani mai tuka motocin alfarma dake zaune a birnin Shanghai, ya samu kudadensa ne ta hanyar saye da sayar da gidaje a birnin Shanghai.

Yana da wani katafaren gidan kasaita mai kimanin dakuna 200 da ya gina a Shanghai kana ya mallaki gidaje a akalla manyan birane biyar a wasu kasashen duniya.

Amma a yayin da yake harkokin kasuwancinsa, ya kuma samu wata kadara da za ta iya ba shi damar samun izinin mallakar gida a Singapore.

Ya ce a bisa dalilai masu yawa, wata dama ce da zai kawo iyalansa.

Amma yayi amanna cewa, saboda dalilan rashin tsaro ne yasa attajirai abokansa da dama suka fi gwammace wa yin rayuwa a wajen kasar ta China..

"Yawancin su na zaton na samu kudi da yawa a nan, amma kila wata rana gwamnati zata sauya manufofinta wanda zai canza komai.'' In ji Louie.

Takardar izinin shiga ta aiki

"Yawancin su na zaton na samu kudi da yawa a nan, amma kila wata rana gwamnati za ta sauya manufofinta wanda zai canza komai."

Louie Huang

Wasu karin masu kudi da yan kasuwar kasar China na neman izinin mallakar gidaje a Amurka ta hanyar saka jari.

A wani taron bita da aka gudanar a wani kasaitaccen ofishi dake nuna birnin Shanghai, an bukaci tare da karfafa gwiwar yan kasuwar China da su zuba jari a tattalin arzikin Amurka.

Tsarin bayar da takardar izinin shiga ta EB-5, wani shiri ne na zuba jari kan samun izunin mallakar gida, bayar da takardar iznin zama, muddin zuba jarin ya samar da akalla ayyuka goma.

Louie Huang dai ya yi amanna cewa iyalansa za su karu da wannan tsari na samun izinin zama a kasashen waje.

Akwai damuwa game da yanayin tsarin rayuwa, hakan ta sa attajirai ke neman samun wuri mai kyau da kuma ingantaccen ilmi ga 'ya'yansu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.