BBC navigation

Shugaba Zuma ya gittawa kwamitin bincike sharadi

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:14 GMT

Ma'akatan ma'adanan da 'yan sanda suka kashe

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya shatawa wani kwamitin bincike na shari'a game da kisan da aka yi a makon jiya a mahakar ma'adinai ta Marikana sharuddan gudanar da ayyukansa.

Alkalai uku ne za su nazarci halayyar kamfanin da ya mallaki mahakar ma'adinan, Lonmin, da ’yansandan kasar wadanda suka harbe mutane talatin da hudu da kungiyoyin kwadago da kuma gwamnati.

A cewar shugaban na Afirka ta Kudu, “Kwamitin zai kammala aikinsa a cikin watanni hudu, ya kuma mika rahotonsa na karshe a cikin wata daya da kammala aikinsa”.

Masu suka sun ce Mista Zuma ya yi jinkiri wajen mayar da martani game da mace-macen, kuma kamata ya yi binciken ya nazarci baki dayan ma'aikatar hakar ma'adinai.

Alkalin da zai jagoranci binciken ya shaidawa BBC cewa zai dauki mataki idan aka yi kokarin yin katsalandan na siyasa a aikin kwamitin nasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.