BBC navigation

Mutane 31 sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa a Nijar- Majalisar Dinkin Duniya

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:54 GMT
Jamhuriyar Nijar

Mutane sama da dubu dari sun rasa matsugunan su a Nijar

Ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya a Nijar ya ce akalla mutane talatin da daya sun rasu, a yayinda wasu fiye da dubu dari suka rasa matsugunan su sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a kasar cikin tsakiyar watan Yuli.

Yankin Dosso shine inda lamarin yafi kamari, inda mutane dubu sabai'n su ka rasa matsugunan su.

A birnin Yamai kuma sama gidaje dubu da dari biyu sun ruguje, sannan mutane sama da dubu ashirin da hudu ne su ka rasa matsuguni

Wakilin BBC a Nijar yace adadin zai fi haka a nan gaba, saboda wasu gidajen fiye da dubu daya su na kan hanyar su ta rushewa, kasancewar a cikin ruwa suke

Galibi dai, makarantu ne akai amfani da su wurin baiwa mutanen da su ka rasa matsugunan su mafaka, kodayake gwamnati tace za tai kokarin kafa tantinan saka jama'a

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.