BBC navigation

Akwai yiwuwar amfani da karfin soji a Mali, in ji Jonathan

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:19 GMT

Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce idan tattaunawar da ake yi da kungiyoyin Islama da ke tayar da kayar-baya a arewacin kasar Mali ta ci tura, za a dauki matakin soji a kansu .

Shugaba Jonathan, wanda ya bayyana hakan a lokacin ganawar da ya yi da shugaban Senegal, Macky Sall a Dakar, ya kara da cewa kasashen yammacin Afirka za su nemi goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya kafin su aike da dakarunsu kasar ta Mali.

Shugaban Najeriyar ya hakikance cewa dole ne yanayin siyasar Bamako, babban birnin kasar Mali ya inganta idan ana son warware matsalar rikice-rikicen da ke addabar arewacin kasar.

A cewarsa, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, wato ECOWAS ta aike da wata tawagar zuwa Bamako don ganawa da sabuwar gwamnatin hadakar kasar, da zummar duba korafe-korafen da wasu yankunan kasar suka yi cewa ba a damawa da su a harkokin kasar.

Jonathan ya ce bayan hakan ne kuma za a fara tattaunawa a kan wadanda ya kira masu tayar da kayar-baya da ke arewacin Mali.

Shugaba Jonathan ya amince cewa kasashen yammacin Afirka kadai ba za su iya shawo kan rikicin arewacin Mali ba.

Ya kara da cewa kasashen biyu, watau Najeriya da Senegal sun tattauna a kan yadda za su bunkasa tattalin arzikinsu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.