BBC navigation

Zuma ya zayyana sharudan bincike

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:04 GMT

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya shata sharuddan wani binciken shara'a da za a yi game da kisan da aka yi makon da ya wuce a mahakar ma'adinai ta Marikana.

Alkalai uku za su nazarci halayyar masu wurin hakar ma'adinan, Lonmin, da 'yan sandan Afrika ta Kudu wadanda suka harbe mutane talatin da hudu a wajen mahakar ma'adinan da kungiyoyin kwadagon da kuma Gwamnati.

An dai soki Mr Zuma game da rashin mayar da martaninsa kan kisan cikin hanzari. Anyi addu'o'in tunawa da mamatan a ko'ina cikin kasar Afrika ta Kudun.

Tuni dai tsohon jagoran matasa na jam'iyyar ANC, Julius Malema ya dora alhakin lamarin akan gwamnatin shugaba Zuma.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.