BBC navigation

Sabon yunkurin taimakawa 'yan tawayen Syria

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:37 GMT

'Yan tawayen Syria

Shugabannin Burtaniya da Amurka da Faransa sun sake yin wasu sababbin alkawura na karfafa goyon bayan da suke bai wa 'yan adawa a kasar Syria.

Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin da suka yi wata tattaunawa ta wayar tarho.

Wani kakakin Firayim Ministan Burtaniya ya ce kasashen sun amince cewa ya kamata a samu kwakkwarar adawa a Syria.

A cewarsa, shugabannin sun tattauna a kan yadda za a samarwa 'yan adawar Syria tallafin da ba na makaman yaki ba ne, kamar yadda gwamnatin Brtaniyar ta sanar a baya.

A farkon watan da muke ciki ne kasashen suka tabbatar cewa za su taimakawa 'yan tawayen Syria da magunguna da kuma tauraron dan adam.

David Cameron ya shaidawa shugaba Obama cewa, ya amince da gargadin da ya yi cewa idan gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba a yakin da take yi da 'yan tawaye, lallai Amurka da Burtaniya za su sauya tunaninsu a kan yadda suke tunkarar rikicin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.