BBC navigation

Kotu ta yankewa Andres Breivik hukuncin dauri

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 11:50 GMT
Anders Behring Breivik

Anders Behring Breivik

Wata kotu dake zamanta a Norway ta bayyana Andres Behring Breivik a matsayin mai cikakken hankali.

Kotun kuma ta yanke masa hukuncin shekaru ashirin da daya a kurkuku.

Anders ya amince da kisan mutane 77 tare da raunata wasu 240 a sakamakon bam din daya saka a birnin Oslo da kuma bude wutar da yayi da bindiga a kan wasu matasa da ke taron jam'iyya wani tsibiri a bara.

Anders ya dage cewa yana da hankali kuma ya ki amincewa ya aikata laifi, inda ya yi ta kokarin bada hujjar kai hare-haren da cewa dole ne saboda a dakatar da maida kasar Norway ta Musulmai.

Masu gabatar da kara dai sun bukaci ace bashi da hankali.

Alkalai biyar ne bakinsu ya zo daya wajen yanke hukuncin cewa Breivik na da hankali.

An same shi da laifin ta'addanci da kuma kisa, inda aka yanke masa hukuncin shekaru ashirin da daya a gidan kaso.

Sai dai za a iya tsawaita zamansa a kurkuku nan gaba, idan ana ganin zai cigaba da zama barazana ga al'umma.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.