BBC navigation

Dan bindiga ya bude wuta a ginin Empire State, a Amurka

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:07 GMT
Ginin Empire State, a New York

Ginin Empire State, a New York

Mutane biyu ne aka kashe, wasu takwas kuma suka jikkata, a sakamakon wata musayar wuta, kusa da ginin dogon benen nan mai hawa sama da dari, dake samun 'yan yawon bude ido, wato Empire State Building a birnin New York.

Wani dan bindiga ne ya bude wuta, inda ya halaka mutum guda , kafin daga bisani shi ma 'yan sanda su bude masa wuta, su halaka shi.

Magajin garin New York, Michael Bloomberg ya ce mai yuwuwa wasu daga cikin wadanda aka jikkata sun samu rauni ne, sakamakon harsasan 'yan sanda da suka same su; ya jaddada cewa babu daya daga cikin su da ransa ke cikin hadari.

An ce sunan dan bindigar, John Jeffrey Johnson, wanda ke yayi aiki a wani shago sayar da sutura, amma aka ya rasa aikin nasa kimanin shekara guda da ta wuce.

Shi ma mutumin da ya bindige din, tsohon abokin aikinsa ne.

Wani bangare na titin Fifth Avenue, da ma wasu titunan sun kasance a rufe.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.