BBC navigation

Neil Armstrong ya rasu

An sabunta: 25 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:11 GMT

Neil Armstrong

Wani labari da muka samu yanzu na cewa, kafafen yada labaru a Amurka sun ce mutumin da ya fara sauka a kan duniyar wata, Neil Armstrong ya rasu, yana da shekaru tamanin da biyu.

An yi masa aikin tiyata kwanakin baya a zuciyarsa.

Yayi tafiya a duniyar wata ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 1969, inda ya bayyana lamarin da cewa, wannan wani mataki ne karami, amma mai girman gaske ga bil'adama.

A watan Nuwambar da ya gabata ne dai ya samu lambar yabo mafi girma ta majalisar dokokin Amurka,

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.