BBC navigation

Dan Sama Jannatin Amurka farko Neil Armstrong ya rasu

An sabunta: 26 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:14 GMT
Neil Armstrong

Neil Armstrong, Dan Sama Jannatin Amurka na farko da ya fara taka duniyar wata

Mutumin nan na farko da ya fara takawa a doron duniyar wata,Neil Armstrong, ya mutu yana da shekaru 82, kamar yadda bayanai daga iyalansa suka nuna.


A cikin farkon wannan watan ne dai aka yi masa aiki a zuciyarsa, sai dai ba a bayyana a inda ya rasun ba.

Bayanan da suka fito daga iyalan Mr Armstrong din sun kuma ce ya mutu ne sakamakon matsalar da ya samu bayan tiyatar da aka yi masa a zuciya a farkon watan nan.

A matsayinsa na Kwamandan tawagar jirgin yan sama jannatin nan ''Kumbo Apollo 11'', Armstrong lokacin da ya fara taka tafin kafarsa a kan dandagaryar duniyar wata a ranar 20 ga watan Yulin shekara ta 1969,, ya furta wasu kalamai da ba za a iya mantawa da su ba inda ya ce '' taku kadan na mutum; wani babban ci gaba ne ga bil adama''.

Bayan ya kammala aikin sa a matsayin matukin jirgin ruwa, Neil Armstrong yayi karatu a fannin koyon aikin injiniyan jirginn sama, ya kuma tuka kananan jiragen yaki lokacin yakin Korea a shakara ta 1950, and joined the US space programme in 1962,kafin ya shiga aikin binciken a wani bangare na Hukumar Binciken Sararin Samaniya na Amurka, NASA.

An kuma zabe shi a matsayin dan sama jannatin da tawagarsa ta zama ta farko da ta fara zuwa da kumbo biyu kan duniyar wata.

Gwarzon Amurka

An dai bayyana Neil Armstrong a matsayin gwarzo, mai kwazo da kaifin basira, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga aikin ci gaban kasa.

Yayinda yake bayyana yabawarsa, shugaba Barak Obama ya ce, Armstrong na daga cikin mashahuran gwarzayen Amurka, ba wai a lokacinsa ba ma, a koda yaushe, wanda kuma ya kawo ci gaban jama'a da ba za a iya mantawa da shi ba.

Takwarorinsa 'yan sama jannati na tawagar aikin 'Kumbo Apollo 11' suma suna mai tunawa da ci gaban da ya kawo, sun mai kwatanta shi da gwarzon mutum mai kawaici da kwazo.

Ba kamar sauran yan sama jannati ba, Neil Armstrong bai shiga siyasa ba, ya koma karatu ne, har ya zama Shaihin malamin Jami'a. Ba kuma kasafai ya kan fito a bainar jama'a ba, amma kuma a cikin shekara ta 2010 ya bayyana a wani babban taro inda yake suka game da shirin shugaba Obama na zaftare kudaden tallafi ga sufurin da bai shafi sararin samaniya ba.

Iyalan Neil Armstrong dai sun ce za su yi jimamin mutuwar mutumin kirki, amma kuma ta wani gefen za su yi bikin murnar yadda ya tafiyar da rayuwarsa mai kyau, wanda kuma suke fatan zai zama misali ga yan baya, na su bautawa jama'a fiye da kan su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.