BBC navigation

Afghanistan: ana bincike akan kisan fararen hula

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:20 GMT
Taswirar Afganistan

Taswirar kasar Afganistan


Jami'an kananan hukumomi a Lardin Helmand dake Afganistan sun ce fararen hula kimanin goma sha bakwai ne aka fille wa kawuna , kana kuma an hallaka kimanin sojojin Afgnistan goma a wani hari na daban.

Fararen hular sun mutu ne a gundumar Musa Qala , dake kudancin gundumar Helmand a daren jiya Lahadi, suma kuma sojojin goman a nan ne aka hallaka su, lokacin da masu tada kayar bayan suka kai hari kan shingen binciken jami'an tsaro a ranar a daren Lahadin.

Har ila yau an bayyana rahoton cewa wani sojan Afganistan ya hallaka sojojin kasashen waje biyu a yau Litinin a gabashin Lardin Laghman.

Makarkashiya

Harin da aka kai kan sojojin goma ya faru ne a gundumar Washir, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar sojojin Afganistan hudu, yayinda akalla biyar suka bata, kana babu tabbacin ko sace su aka yi ko kuma sun bi maharan ne a kashin kan su.

Sai hukumomin sun ce akwai makarkashiya game da kai wannan hari, sun kuma ce ana kan gudanar da bincike.

Lamarin da ya faru a lardin Langhman daya daga cikin hare-haren da jami'an tsaron Afganistan suka kai kan dakarun kasashen waje ne a cikin wannan watan.

Har yanzu dai ba a gano ko daga wace kasa sojijin da aka hallaka suka fito ba.

Rahotanni dai sun ce Jami'an tallafawa kan harkokin tsaro na kasa da kasa ISAF, sun mayar da martani inda suka hallaka maharin.

Akalla Jami'an tsaron na ISAF arba'in da biyu ne dakarun Afganistan suka hallaka a cikin wannan shekarar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.