BBC navigation

Kenya: ana tarzoma akan kisan malami

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:05 GMT

Marigayi Aboud Rogo Muhammed

Tarzoma ta barke a birnin Mombasa na Kenya bayan an bindige wani malamin addinin Musulunci da ake zargin yana goyon bayan masu tsattsauran ra'ayi na Somalia.

'Yan sanda sun ce malamin, Aboud Rogo Mohammed, da mai dakinsa suna cikin tafiya a motarsu sai wani dan bindiga ya bude musu wuta.

'Yan sandan sun kuma musanta rahotannin da aka ba da tun da farko cewa su ne suka bindige malamin.

An kashe mutum guda an kuma jikkata da dama a hatsaniyar da ta biyo baya; an rurrufe shaguna an kuma kwashi ganima a wata majami'a.

An kuma kwashe ababen hawa daga kan tituna abin da ya sa matafiya suka rasa ta yi.

Malam Aboud Rogo na cikin jerin mutanen da majalisar dinkin duniya ta sanyawa takunkumi bisa zarginsa da bada tallafin kudi ga kungiyar Al-shabaab.

A farkon shekarar nan ne 'yan sandan Kenya suka tuhume shi da laifin mallakar bindigogi, tare da kuma kasancewa mamba a kungiyar Al-Shabaab, abinda ya sabawa dokar kasar ta Kenya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.