BBC navigation

Shugaban Syria ya zargi kasashen waje da makarkashiya

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:53 GMT
Shugaban Syria Bashar al Assad

Shugaban Syria Bashar al Assad ya zargi kasashen waje da yin makarkashiya

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya danganta rikicin dake faruwa a kasar da wata makarkashiya kan daukacin yankunan daga kasashen waje.

Mr Assad din ya furta hakan ne bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce ranar Asabar ita ce mafi muni a Syria, tun da aka fara rikicin nuna kin jinin gwamnati a kasar.

'Yan adawa masu Fafitika sun ce an samu gawawwakin mutane da dama a garin Daraya,dake wajen Damascus babban birnin kasar ta Syria.

Masu fafitikar sun ce dakarun gwamnati da na yan tawayen sun yiwa mutane sama da dari uku kisan kiyashi lokacin cin zarafin da ya abku a yankin Daraya, dake wajen Damascus babban birnin kasar.

A wasu wurare a Aleppo birnin mafi girma a kasar, kana a birnin Daraa da ke kudancin kasar kuma dakarun gwamnati na ci gaba da lugudan wuta ta sama kan yankunan da yan tawaye suka karbe.

Wani rahoto kuma da ba a tabbatar da shi ba daga masu fafitikar ya ce an samu gawawwakin mutane fiye da dari biyu a gidaje da wasu wurare, da a bisa dukkan alamu dakarun gwamanti ne suka hallaka su yayin kai samame gida gida.

Sai dai wannan rahoton da aka gabatar a gidan talabijin na Addonia, mai goyon bayan gwamatin Syria ya dora alhakin kisan kan yan tawaye.

Wasu matan a garin Darayya, basu ma tabbaatar da ko su wanenen suka kai musu harin ba.

''Ban sani ba, ina son zuwa birnin Damascus da mijina da yarana ne, kawai sai na samu kai na cikin wannan yanayi.Ban san inda yarana suke ba, ban san komai ba banda samun raunin da na yi.''

''Ba mu san inda muka nufa ba, kana bamu san ta inda suka bullo ba.Lokacin da muka zo nan mun ji alamun muna tudun muun tsira, mun bar gidajenmu saboda sun fada mana cewa dakarun tsaro zasu zo su hallaka mu.Wasu mazaje ne dauke da makamai sun shaida mana.''

Shugaban na Syria Bashar al Assad dai ya yi alwashin murkushe duk wata makarkashiya daga kasashen wajen.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.