BBC navigation

Kwamitin Sulhu na bukatar garambawul —Hollande

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:31 GMT
Francois Hollande

Shugaba Francois Hollande na Faransa

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce kiki-kakar da ake samu a Majalisar Dinkin Duniya dangane da batun Syria ta nuna cewa akwai bukatar yin garambawul ga Kwamitin Sulhun majalisar.

A jawabinsa na shekara-shekara ga jakadun Faransa, Mista Hollande ya ce hawa kujerar na-kin da Rasha da China ke yi ya sa Majalisar ta yi rauni har ta kai tana fuskantar hadarin zama saniyar ware, ko ta kasa wani katabus.

“Tambayar da ake yi a yau ita ce anya mambobin kwamitin za su iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, su kyale majalisar ta yanke shawara? Saboda hawa kujerar na-ki ka iya kaiwa ga mayar da majalisar saniyar ware”, inji Mista Hollande.

Ya kuma yi kira ga ’yan adawar Syria da su kafa gwamnatrin hadin kasa wacce ya ce Faransa za ta amince da ita.

Hakazalika ya yi gargadin cewa idan kasar ta Syria ta kuskura ta yi amfani da makamai masu guba to za ta jawo tsoma-bakin sojin kasashen waje.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.