BBC navigation

Yunkurin rage hauhawar farashin kayan abinci

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:17 GMT

Kasuwa

Mahalarta taro a kan sha'anin ruwa a kasar Sweden sun shaidawa 'yan siyasa da kwararru kan sha'anin noma a duniya cewa dole ne su rage yawan abincin da ake barnatarwa idan ana son tsayar da hauhawar farashin kayan abincin.

Mahalarta taron sun ce kimanin daya bisa uku na abincin da ake nomawa ba ya isa ga jama'a.

Shugaban Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, Jose Graziano Da Silva, ya yi kira da a dauki mataki na hadin-gwiwa tsakanin kasashen duniya masu arziki wadanda ke noma kimanin kashi casa'in bisa dari na abincin da farashinsa ke hauhawa.

A cewarsa, hakan zai rage hauhawar farashin kayan abinci a duniya.

A kwanakin baya, wani rahoto da kungiyoyin agaji guda biyu suka fitar ya nuna cewa fiye da mutane miliyan goma sha takwas ne a yankin Sahel da ke yammacin Afurka ke fama da matsalar rashin abinci ta din-din-din.

Rahoton, wanda kungiyoyin World Vision da Save the Children suka fitar, ya kara da cewa fiye da yara miliyan guda ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar yunwa.

Kungiyoyin sun ce ko da a shekarar da ba a fuskanci matsalar rashin abinci ba, yara fiye da dubu dari biyu ne suka mutu a yankin saboda rashin samun abinci mai gina jiki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.