BBC navigation

Me ya sa shugabannin Afrika ke mutuwa a kan mulki?

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 13:27 GMT
Gawar Firai ministan Habasha, Meles Zenawi

Gawar Firai ministan Habasha, Meles Zenawi

Abu ne da ba kasafai yake faruwa ba, shugaban kasa ya mutu a yayin da yake jan ragamar mulki.

Sai dai tun shekarar 2008 hakan ya yi ta faruwa har sau 13 a fadin duniya.

Kuma goma daga cikin shugabannin da suka mutu a kan mulki sun fito ne daga nahiyar Afrika.

Me ya sa hakan ya fi yawa a nahiyar ta Afrika?

Taron mutane dauke da kendira ne suka baibaye gawar shugaban Habasha Meles Zenawi, a yayin da ake wucewa da gawar ta Adis Ababa, kuma ya mutu ne yana da shekarau 57, bayan doguwar rashin lafiya.

A watan Yuli ne kuma dubun dubatar mutanen Ghana suka halarci jana'izar shugaban kasar, John Atta Mills, wanda ya mutum yana da shekaru 68 a duniya.

Watanni hudu da suka gabata ne, aka shiga makoki a Malawi don mutanen kasar su sami damar halartar jana'izar shugaba Bingu wa Mutharika, wanda ya mutu sakamakon ciwon zuciya yana da shekaru 78.

A watan Janairun shekarar 2012 ne kuma shugaban kasar Guinea Bissau, Malam Bacai Sanha ya mutu a wani asibitin sojoji dake Faransa, bayan doguwar rashin lafiya, yana da shekaru 64.

Hakan na nufin shugabannin Afrika hudu ne suka mutu a wannan shekarar kadai.

Tunanin 'yan jarida

Abin damuwa ne ga mutanen kasashensu, abin bakin ciki ga iyalansu, amma su fa masu aiko da rahotanni me suke gani game da mutuwar ta su?

Mai aiko da rahotanni ga shafin internet na Daily Maverick na Afrika ta Kudu, Simon Allison ya bayyana cewa " An yi ta kira na ta waya da daddare cewa ga wani shugaban Afrika ya mutu. Na yi tambaya shin me ya sa shugabannin Afrika ke mutuwa?"

Tambayar dai ta sa ya duba tsawon rayuwar shugabannin.

Inda ya kara da cewa " Ina duba 'yan shekaru kafin yanzu sai na ga jerin shugabannin da suka mutu suna da yawa."

"Shugabannin Afrika kafin a zabe su, sun yi rayuwa cikin wahala a baya, kuma hakan zai shafi tsawon rayuwarsu a lokacin da suke kara girma."

Dr. Goerge Leeson na jami'ar Oxford

Tun shekarar 2008 shugabannin Afrika goma ne suka mutu a kan mulki.

Hakika da gaske ne shugabannin Afrika sun fi mutuwa a kan mulki fiye da kowacce nahiya.

A cikin wannan lokaci dai shugabanni uku ne kawai suka mutu a sauran sassan duniya.

Kuma su ne shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Il, shugaban kasar Polland, Lech Kaczynski wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama da kuma shugaba David Thomson na Barbados wanda ke da cutar sankara.

A bayyane yake cewa shugabannin Afrika sun fi mutuwa a kan karagar mulki saboda tsufa fiye da takwarorinsu na wasu nahiyoyi.

Bayanin da Simon ya fi amincewa da shi kenan.

Kuma ya yi amannar cewa 'yan Afrika sun fi son dattawa a matsayin shugabannin kasa, saboda al'adar dake tattare da girmama manya a yawancin kasashen nahiyar.

Dattijai

Hakika shekaru 61 ne matsakaita na shugabanin Afrika da kuma a nahiyar Asiya.

A nahiyar Turai kuwa shekaru 55 su ne matsakaita, yayin da a kudancin Amurka, shekarun su ne 59

Sai dai wani abin dubawa a nan shi ne tsawon rayuwar al'umma, wanda nahiyar Afrika ke da mafi karanci a kan nahiyar Turai, yakin Latin Amurka da Asiya.

Hakan ya biyo bayan yawaitar wasu cututtuka kamar HIV/Aids da rashin kyakyawan tsarin kula da marasa lafiya wanda ke janyo yawan mace-mace a gurin haihuwa.

Sannan talauci a lokacin kuruciya da kuma a farkon rayuwa na tasiri na tsawon lokaci, kamar yadda Dr. Goerge Leeson na jami'ar Oxford ya bayyana.

"Shugabannin Afrika kafin a zabe su, sun yi rayuwa cikin wahala a baya, kuma hakan zai shafi tsawon rayuwarsu a lokacin da suke kara girma." In ji Dr. Leeson.

" Da zarar sun kama mulki, duk da cewa rayuwarsu ta fi ta mutanen kasa ingantuwa nesa ba kusa ba, wanda hakan ka iya kara musu tsawon kwana fiye da 'yan kasa, sun riga suna tare da wuyar da suka sha a baya kuma zai shafi rayuwarsu a wani lokaci."

Kodayake ba dukkan shugabannin Afrika ne suka sha wuya a rayuwar su ta baya ba.

Amma akwai wasu dalilan da ya kamata a duba kamar siyasa.

Shi shugaban Afrika na son dawwama a kan mulki har sai ya mutu, sai dai ba lallai ba ne hakan ya zama ainihin abin da ke faruwa.

"Haka batun yake idan ka yi la'akari da shugabanni kamar Omar Bongo da Conte da kuma Gaddafi" A cewar Simon.

Gawar Firai ministan Habasha, Meles Zenawi

Gawar Firai ministan Habasha, Meles Zenawi

Ya kara da cewa "Dukkansu sun yi mulkin kama-karya kuma ba su so barin mulki da kashin kansu ba, amma ba haka batun yake ba ga sauran, misali Meles Zenawi ya dade yana mulki, amma kuma shekarunsa 57 ne kawai, haka ma sauran duk suna wa'adin mulkinsu ne ba su ma yi nisa ba tukuna."

Yana da muhimmanci a yi la'akari da cewa an duba wannan batu ne tun daga shekarar 2008, kuma ta iya yiwuwa lissafin mutuwar a wannan lokaci akwai kuskure.

Amma koma menene ke faruwa, yawan mutuwar na janyo rashin tabbas.

Mutuwa a kan karagar mulki na janyo gibi, wanda hakan na da hatsari.

Simon ya yi nuni da cewa " Duba abin da ya faru a Guinea-Bissau, lokacin da Sanha ya mutu, juyin mulki ya biyo baya. Wannan na jefa naiyar Afrika cikin wani hali, tun da a tarihi ba ta iya jure gibi a mulki."

Sai dai ya yi imanin cewa akwai kyakkyawar fata.

" Mutuwar shugabanni a kasashen Zambia da Malawi da Ghana da kuma Najeriya ya sa an samu cigaba da mulkin farar hula ba tare da tashin hankali ba. Hakan ina ganin wata alama ce da za ta sa kwarin gwiwa na cigaban Afrika."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.