BBC navigation

Masu gabatar da kara na Faransa za su binciki kisan Arafat

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:27 GMT
Marigayi Yasser Arafat

Marigayi Yasser Arafat

Masu gabatar da kara na kasar Faransa sun bude bincike kan zargin kisan kai, game da mutuwar jagoran Palasdinawa Yasser Arafat.


Matar Mr Arafat ce ta shigar da koke gaban kotu a Faransar cikin watan jiya, bayan wani shirin talabijin yayi zargin cewa an kashe shi ne da guba.


Yasser Arafat ya rasu ne a wani asibitin soja a Faransa a 2004, bayan fama da wata gajeriyar rashin lafiya, aka kuma rufe shi ba tare da binciken musabbabin mutuwarsa ba.


Shirin talabijin din na Al Jazeera, ya ambaci wani masanin kimiyya dan kasar Switzerland yana cewa sun gano burbushin sinadarin polonium mai guba a wasu daga cikin kayayyaki mallakin Mr Arafat.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.