BBC navigation

Colombia na tattaunawa da 'yan tawaye

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:13 GMT

Juan Manuel Santos

Shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos, ya tabbatar cewa gwamnatinsa na tattaunawar sharar fage da babbar kungiyar 'yan tawayen kasar, FARC.

Mista Santos ya yi wannan kalami ne a wani gajeren jawabi da ya yi ta gidan talabijin na kasar.

Ya ce tattaunawa da FARC na daga cikin 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi na neman zaman lafiya ga kasarsa.

Santos ya tabbatar wa 'yan kasar cewa yana tattaunawar ce cikin taka-tsan-tsan da kuma hangen nesa.

Shugaba Santos ya yi waiwaye kan yadda gwamnatin kasar ta gaza yin nasara a tattaunawar da ta yi da kungiyar FARC a karshen shekarun 1990, yana mai cewa gwamnatinsa ta dauki darasi game da waccan tattaunawar.

Ya kara da cewa sojin kasar za su cigaba da tabbatar da tsaronta yayin da ake tattaunawar, inda za su kasance a duk lungunan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.