BBC navigation

Shin Paralympic na da tasiri kan nakasassu?

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:37 GMT
disability

Tawagar jamhuriyar Nijar lokacin da suka isa London

A daidai lokacin da ake fara gasar wasannin Olympics ta nakasassu, sashen Hausa na BBC na gayyatarku domin shiga cikin muhawarar ta musamman gudanar a shafukanmu na sada zumunta.

Muna son jin ra'ayinku kan ko wane sauyi aka samu kan yadda jama'a ke kallon nakasassu tun bayan gasar da ta gabata? Ko wasanni na tasiri kan yadda jama'a ke kallon nakasassu?

Kuna da damar tattaunawa da mutane daga sassan duniya da suka hada da Latin Amurka da Turai da kuma nahiyar Asia.

Sai a kasance tare da mu a shafinmu na Facebook da Twitter. Ga masu bin mu a Twitter sai ku yi amfani da (Hash tag) #paralympics_bbc {watau #paralympics underscore bbc}.

Za mu gudanar da wannan tattaunawa ne yau da rana da misalin karfe 2.00 zuwa karfe 5.00 na yamma agogon Najeriya da Nijar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.