BBC navigation

An kashe fursunoni tara a Gambia

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:33 GMT
Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh

Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh

Kimanin fursunoni tara aka kashe a kasar Gambia, duk da kiraye-kirayen da kungoyoyin kare hakkin Bil-adama da kuma kasashen duniya suka yi na kada a aikata hakan.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce an harbe fursunonin ne da bindiga a ranar lahadin data gabata.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya sha alwashin kashe fursunoni 47 da aka yankewa hukuncin kisa kafin nan da tsakiyar watan gobe.

Kungiyoyin kare hakkin Dan-adam da sauran kasashen duniya sun bayyana matukar damuwarsu, inda suka bukaci Mista Jammeh ya dakatar da kisan.

A makon daya gabata ne, hukumar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta soki hukuncin bayan ta samu labari kwanaki uku kafin a kashe fursunonin.

Mafi akasarin fursunonin dake jiran hukuncin kisa, tsofaffin jami'an gwamnatin kasar ne da kuma manyan sojoji wadanda ke tsare tun shekarar 1994, bayan Mista Jammeh ya karbi karagar mulkin kasar ta hanyar juyin mulki.

Shugabar kungiyar tarayyar turai kan manufofin kasashen waje, Cathrine Ashton ta bukaci kasar ta Gambia ta dakatar da kisan nan take.

Jawabin Sallah.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce akwai mace daya a cikin wadanda a kashe.

Haka kuma ta bayyana wasu laifuka da hada da kisan kai da cin amanar kasa da bore tare da kone-kone da safarar muyagun kwayoyi da mutane hukuncinsu shi ne kisa.

Sai dai har yanzu ba a tantance wane irin laifi wadanda aka kashen su aikata ba.

Tun a lokacin mulkin shugaba Dawda Jawara aka daina yanke hukuncin kisa, amma bayan da Mista Jammeh ya dare karagar mulki a 1995 ya dawo da hukuncin.

A jawabinsa na Sallah ta kafar talabijin din kasar, shugaba Jammeh yace "kafin nan da tsakiyar watan gobe za a kashe duk fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa, babu yadda za a yi gwamnatina ta bari masu aikata manyan laifuka su dami al'umma."

A martani game da hakan, shugaban Jamhuriyar Benin,Thomas Boni Yayi, wanda kuma shi ne shugabancin kungiyar tarayyar Afrika ya aika da ministan harkokin wajen kasarsa zuwa Gambia domin ya gargadi Mista Jammeh cewa kada ya kara aiwatar da hukuncin kisa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.