BBC navigation

Mali ta nemi taimako don yaki da 'yan tawaye

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:29 GMT
Shugaban Mali na riko Diaoncunda Traore da Firayim Minista Cheikh Modibbo Diarra

Shugaban Mali na riko Diaoncunda Traore da Firayim Minista Cheikh Modibbo Diarra

Gwamnatin Mali ta yi kira ga kasashen duniya su taimaka mata ta ga bayan masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama wadanda suka kwace iko da fiye da kashi biyu bisa uku na fadin kasar a farkon wannan shekarar.

Tuni dai shugabnnin yankin suka far gargdain cewa masu tsattsauran ra'ayin, wadanda akasarinsu baki ne za su iya mai da kasar ta Mali wata mafaka irin su Somalia da Afghanistan.

Masu tsattsauran ra'ayin na addinin Islama wadanda ake alakantawa da kungiyar Al-Qa'ida sun kwace iko da arewacin kasar ne tare da taimakon ’yantawaye Azbinawa bayan juyin mulkin da ya hambarar da zababben shugaban kasar a watan Maris.

Bayan da suka sha kasha, wani jami’I a rundunar sojin kasar ta Mali, Kanar Didier Dako, ya ce a halin yanzu dakarunsa sun zaku su sake karbe iko da arewacin kasar.

Kanar din dai yana da tabbacin cewa dakarun nasa za su iya sake kwace arewacin kasar—wanda yanki ne da ya yi girman Faransa—ba tare da taimakon kasashen duniya ba.

'Ba mu da karfin soji'

To amma Ministan sadarwa na kasar, Hammahoun Toure, bai yarda da hakan ba.

A cewarsa, “Ba mu da sojoji da yawa, ba mu da kayan aiki, ba mu da horo, don haka muna bukatar taimako daga waje”.

Masu tsattsauran ra’ayin addinin Islaman da kuma kawayensu Azbninawa na da makamai sosai, wadanda galibi suka samu sakamakon fadadar cinikayyar miyagun kwayoyi da kuma satar mutane a yankin da suke iko da shi.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afrika, wato ECOWAS, wadda ke goyon bayan amfani da karfi domin sake kwace iko da arewacin kasar, ta ce ya kamata duniya baki daya ta damu.

Kasashen duniya dai na fatan cewa sabuwar Gwamnatin hadin kan kasar ta Mali za ta sasanta da ’yantawayen.

To amma wani kakakin gwamnatin kasar ya shaida wa BBC cewa tattaunawa da masu tsattsauran ra'ayi na waje abu ne da sam ba zai sabu ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.